Jihar Gabas ta Tsakiya tsohuwar yanki ce ta mulkin Najeriya.[1] An kirkire ta ne a ranar 27 ga Mayu 1967 daga sashen Gabas kuma ta wanzu har zuwa 3 ga watan Fabrairun 1976, lokacin da aka raba ta zuwa jihohi biyu - Anambra da Imo.[2] Yanzu yankin ya kunshi jihohi biyar; Anambra, Imo, Enugu, Ebonyi da Abia. Birnin Enugu ne babban birnin jihar Gabas ta Tsakiya na lokacin.[3]